Ana zaman makoki a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram sun kai hari garin Difa, inda suka kashe sojojin Nijar guda 48.

Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki 3 sakamakon mutuwar sojojinta 46 da suka rasa rayukansu a wani harin da 'yan kungiyar boko haram suka kai musu a tsibirin Karamga da ke tafkin cadi.

Gwamnatin ta ce za ta kara karfafa matakan tsaro a yankin Difa, tare da samar wa jami'an tsaro ingantattun kayan aiki.

A bangare guda kuma, Amurka ta jajanta wa Nijar game da mutuwar dakarunta, kana ta sha alwashin ci gaba da taimaka wa a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

A watan Fabrairu ne majalisar dokokin kasar ta amince gwamnati ta tura dakaru cikin rundunar hadaka ta kasashen da ke yankin tafkin Cadi domin yaki da Boko Haram.