Shugaba Gnassingbe ya lashe zaben Togo

Image caption Shugaba Gnassingbe ya lashe zaben kasar Togo a karo na uku

Hukumar zabe ta kasar Togo ta sanar da shugaba Faure Gnassingbé a matsayin wanda ya lashe zaben kasar a karo na uku.

Sakamakon da aka fitar na wucingadi ya nuna cewa shugaban mai ci -- wanda ya dare mulkin kasar a shekara ta 2005 -- ya samu fiye da kashi 58 cikin dari na kuri'un da aka kada.

A baya dai dan takarar jam'iyyar adawa, Jean-Pierre Fabre, ya yi kira ga 'yan kasar da su nemi sauyin shugabanci.

A bara mutane suka yi zanga-zanga a Togo inda suka bukaci gwamnati ta gabatar da dokar takaita wa'adin shugabancin kasar zuwa sau biyu kawai.

Dokar kasar Togo dai ba ta iyakance adadin da shugaba zai yi a kan mulki ba.