CAR: Hollande ya ce babu sani ba sabo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin Faransa na aikin kiyaye zaman lafiya a Bangui

Shugaban Faransa Francois Hollande, ya ce babu sassauci kan duk wani jami'in sojan da aka samu na cin zarafin kananan yara a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Rahoton da wani jami'in aikin agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya kwarmata ne, ya nuna cewa ana lalata kananan yara maza da suka bukaci abinci---inda ya ce yana matukar bakin ciki kan gazawar majalisar wajen daukar matakai.

Masu gabatar da kara a kasar Faransar dai na gudanar da bincike kan zargin.

Mr Hollande ya shaidawa manema labari cewa duk wanda aka samu da aikata laifin zai fuskanci hukunci mai tsanani.

"Muddin wasu jami'an soja, suka aikata ba daidai ba a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, to kuwa za a hukunta su daidaita yadda doka ta tanada, ba za mu yi sassauci ba," in ji Hollande.