An hukuntan wadanda suka harbi Malala

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Malala Yousafza tana fafutikar ganin mata sun yi ilimi.

Wata kotu a kasar Pakistan ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan mutanen nan goma da aka kama da laifin harbin Malala Yousafzai, shekaru uku da suka gabata.

Malala -- wacce ke da shekaru 15 a lokacin da aka kai mata harin -- an harbe ta ne a kanta.

'Yan kungiyar Taliban ne suka kai mata harin saboda fafutikar da take yi wajen ganin mata sun nemi ilimi.

A bara ne dai Malala ta zama mutum mafi kankantar shekaru da ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.