Nepal: An gano wani yaro da ransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ceto wani yaro da rai a karkashin baraguzai kwana biyar da girgizar kasar Nepal

Kusan kwanaki biyar tun bayan girgizar kasar da ta auku a Nepal, masu aikin ceto a babban birnin kasar, Kathmandu, sun samu wani yaro dan shekara 15 da ransa a wani kwarmi mai iska a karkashin tulin baraguzai.

Mutane sun yi ta sowa lokacin da aka fito da yaron, kafin a zarce da shi zuwa asibiti.

Jami'ai sun ce zuwa yanzu mutane fiye da dubu biyar da dari biyar ne aka hakikance sun rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar ta ranar Asabar.

Sufeto Rajan Raj Upreti jami'i ne a rundunar 'yan sanda ta Kathmandu, ya kuma ce ana fuskantar wahalhalu a aikin ceton.

"Muna fama da karancin wutar lantarki, shi ya sa ba ma iya amfani da manyan na'urorin tono ko na yankan karfe", a cewar Sufeto Upreti, wanda ya kara da cewa, "A gefe daya muna fama da da wadannan wahalahlu yayin da a daya gefen kuma muke fama da damina".

Kauyukan da ke kusa da tushen girgizar kasar na fama da karancin abinci da ruwnan sha da matsugunai, kuma a cewar Majalisar Dinkin Duniya, za a yi tafiyar kasa ta kwanaki biyar kafin a kai garesu.

Karin bayani