An kubutar da karin mutane 160 daga Sambisa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Nigeria na murnar kawar da 'yan Boko Haram daga wasu garuruwa

Rundunar sojin kasa ta Nigeria ta ce ta kubutar da karin mutane fiye da 160 daga dajin Sambisa inda ya kasance maboyar 'yan Boko Haram.

Mukaddashin kakakin sojin kasar, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka a hirarsa da BBC ya bayyana cewar a yanzu haka ana tantance mutanen domin kai su amintaccen wuri, inda za a kula da su.

Kuka-sheka ya ce "Muna kokarin tattara adadin mutanen da aka ceto. Amma dai tabbas akwai mata fiye da 60 da kuma maza da 'yan mata da yara kanana fiye da 100 da aka kubutar."

Rundunar ta kara da cewa dakarunta sun kashe kwamandoji da mayakan kungiyar Boko Haram din da dama sannan suka lalata motoci biyu masu sulke, da wasu motocin biyu masu dauke da bindigogin kakkabo jiragen sama, da motoci kirar Hilux da dama.

A ranar Talata ne dai rundunar tsaron kasar ta ba da rahoton kubutar da mata 93 da 'yan mata 200 daga dajin na Sambisa.

Sai dai kuma hukumomin tsaron sun ce ba ko daya daga cikin 'yan matan nan da aka sace daga makarantar Chibok shekara guda da ta gabata.