Nigeria: An kashe mafarauta sama da 50

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hoton gawarwakin wasu tarin mutane da mahara suka taba kashewa a jihar Zamfara ke nan

Wasu mutane da ake zaton 'yan fashi ne sun hallaka mafarauta sama da 50, wadanda suka yi gangamin farauta a dajin Sammaje da ke da iyaka da jihohin Zamfara da Kebbi da Naija da Kaduna.

Wasu rahotanni sun ce 'yan fashin sun farma mafarautan ne, ranar Laraba da rana, bisa zargin cewa sun kai musu hari ne a maboyarsu a dajin .

Dajin na daga wani bangare na gandun dajin Kuyan-bana mai iyaka da jihohin Kebbi da Kaduna da Naija da Zamfara.

Rahotannin farko da BBC ta samu sun ce lamarin ya faru ne a yankin dajin na Sammaje a bangaren jihar Zamfara.

Amma kuma daga baya kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Sunusi Amiru, wanda da farko ya ce ba shi da labarin lamarin ya ce, ya faru ne a yankin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Rahotannin sun ce 'yan fashin sun bude wa mafarautan wuta ne.