Colombia: An daure tsohuwar shugabar leken asiri

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Shugaba kasar Colombia Juan Manuel Santos

Kotun kolin Colombia ta yanke wa tsohuwar shugabar hukumar leken asiri ta kasar wadda aka rushe hukuncin zaman kaso na shekaru 14, saboda rawar da ta taka wajen satar bayanan wayoyin 'yan adawa da alkalai da 'yan jarida.

Mai shari'a Fernando Castro ya ce an yankewa Maria el Pilar Hurtado Afanador hukuncin ne da biyan tarar dala 644,350, sannan an haramta mata rike duk wani mukami na gwamnati har abada.

Tsohuwar jami'ar ta yi aiki ne a karkashin tsohon shugaban kasar Alvaro Uribe, wanda ya musanta cewa yana da masaniya a kan satar bayanan.

An kuma yanke wa wani na hannun damar Mista Uribe hukuncin daurin talala na shekaru takwas saboda samun shi da aka yi da laifin neman mallakar bayanan da aka tattara ta haramtacciyar hanya.