An haramta saka Hijabi a jamhuriyar Kwango

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daga mako mai zuwa matan Musulmi a Kwango za su daina saka Hijabi

Jamhuriyar Kwango ta haramta saka hijabi ga al'ummar Musulmi a cikin kasar.

Hukumomi a kasar sun kuma haramta wa Musulmin da suka shigo kasar daga makwabtan kasashe, kwana a cikin masallaci.

Wannan na daga cikin matakan da hukumomin suka ce sun dauka na murkushe ayyukan masu matsanancin ra'ayin addinnin Musulunci.

Dubban al'ummar Musulmi daga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya suna kwana a masallatai a Kwango inda suka neman mafaka bayan rikicin da aka yi a kasarsu.

Al'ummar Musulmi a Kwango Brazzaville ba su wuce kashi biyar cikin 100 ba.

Kwango ce kasa ta farko a wannan yankin da ta dauki wannan matakin.