Ghana ta haramta shigo da kaji daga Burkina Faso

Image caption Murar tsuntsaye ta kashe dubban kaji a Burkina Faso

Gwamnatin Ghana ta haramta shigowa da kaji ko namansu daga kasar Burkina Faso zuwa cikin kasarta.

Hakan ya biyo bayan barkewar cutar murar tsuntsaye a Burkina Faso din.

Sanawar da hukumomin Ghana suka fitar ta bukaci mahukunta a yankin arewacin kasar da su sa ido sosai domin ganin ba'a samu barkewar cutar a cikin kasar ba.

Gwamnatin ta kuma bukaci al'ummar kasar su dafa kaji ko kwoi da kyau kafin a ci.

A farkon wannan watan ne gwamnatin Burkina Faso ta tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye a cikin kasar abin da ya janyo mutuwar kaji da dama.