Mutane a Nepal na matukar bukatar agaji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane sun shiga cikin tasku sakamakon girgizar kasar

Mutanen da ke zama a kauyukan zagayen cibiyar mummunar girgizar kasa a Nepal sun ce ba su samu kome na taimako ba, kusan mako guda bayan bala'in.

Mazauna wani karamin kauye sun ce dole suke cin bashin shinkafa daga wani gari da ke kusa da su.

Wani dan jaridar da ya je kauyen, ya ce kusan dukanin gidaje sun ruguje.

Ya ga irin wannan barna a sauran al'umomin ma.

Gwamnatin Nepal ta yi kira ga gwamnatocin kasashen waje da su kara aikewa da jirage masu saukar ungulu domin kai kayan agaji zuwa wurare masu nisa da ke yankunan tsaunuka.

A halin yanzu dai mutane fiye da 6,200 ne dai aka san sun mutu sakamakon girgizar kasar.