Mutane 6,200 sun mutu a Nepal —Hukumomi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirage masu saukar ungulu ne kadai ke iya kai agaji ga mabukata

Hukumomi a Nepal sun ce yawan mutanen da aka san cewa girgizar kasar ranar Asabar ta hallaka ya kai dubu shida da dari biyu, yayin da wasu mutanen dubu goma sha uku kuma suka jikkata.

An zakulo mutane biyu da ransu daga cikin baraguzai jiya Alhamis, amma fatan samun wasu masu nisan kwanan na kara dusashewa.

Jami'ai sun ce 'yan kasar ta Nepal fiye da dubu dari ne ke aikin ceto da ba da agaji.

Mai yiwuwa rashin kyawun yanayi ya hana jiragen sama masu saukar ungulu isa wuraren da abin ya shafa.

Gwamnatin kasar ta Nepal ta yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya su agaza da karin jirage masu saukar ungulu, wadanda da su ne kawai ake iya aikewa da kayan agaji, da kuma kwashe mutane daga kauyukan da ke kan tsaunuka.

Karin bayani