Mun san kamen mutanenmu a Saudiyya —Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi zargin jami'an Saudiyya na cin zarafin mutanen da suka kama

Hukumomin Najeriya sun ce suna sane da yadda jami'an gwamnatin Saudiyya ke kamen mutanen da ke zaune a kasar ta Gabas ta Tsakiya ba bisa ka'ida ba.

Wadansu 'yan Najeriya da ke zaune a Saudiyya dai sun yi korafin cewa yayin wannan kame wani lokaci sai mutum yana zaune a gida da iyalansa sai a balla kofa a shiga.

Jakadan Najeriya a birnin Jeddah, Ambasada Ahmad Umar, ya shaida wa BBC cewa sun yi wa hukumomin kasar ta Saudiyya nuni da bukatar sara ana duba bakin gatari.

"Mun daga wannan magana da su hukumar Saudiyya, mun ce ba shakka ko wacce kasa tana da hurumin zartar da doka bisa yadda take so. Amma duk da haka wajen aiwatarwa, ya kamata ayi la'akari da 'yanci, da kuma kare mutunci na wanda za a kama".

Hukumomin na Saudiyya dai sun kara kaimi wajen kamen 'yan kasashen wajen da ke zayune a can ba bisa ka'ida ba ne yayin da watan azumi ke kara matsowa.

Sai dai jakadan na Najeriya ya ce tun shekarar 2013 Saudiyyar ta tsananta kamen saboda dalilai na tsaro.

Ya kuma ce tun a lokacin, bayan da Saudiyya ta sanar da su aniyarta ta kame wadanda wa'adin takardunsu suka kare, gwamnatin Najeriya ta nemi 'yan kasar sun je a mayar da su gida, amma kalilan ne daga cikin su suka amsa kiran.