Nigeria: Sojoji sun kai mata 300 sansani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mata da yara kusan 300 aka kai sansanin da ke birnin Yola na Jihar Adamawa

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta kai kashi na farko na mata da 'yan matan da ta ce ta ceto daga mayakan kungiyar Boko Haram wani sansanin 'yan gudun hijira.

Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA wacce ta kafa sansanin, Dokta Sani Datti, ya ce mutanen sun isa sansanin a galabaice.

"Da ka kalle su za ka ga sun galabaita; za ka ga sun dade ba su yi wanka ba", inji Dokta Datti, wanda ya kara da cewa, "Suna saukowa abin da muka fara musu shi ne muka tare su da abinci".

A cewar sojojin na Najeriya, matan da 'yan matan da kuma kananan yara su kusan dari uku sun yi kwanaki uku suna tafiya daga Dajin Sambisa na yankin arewa maso gabas.

Kusan mutane dari bakwai ne aka ba da sanarwar kubutar da su a wannan makon, yayin da rundunar sojin kasar ke ci gaba da yunkurin kakkabe mayakan kungiyar Boko Haram daga dajin na Sambisa.

Har yanzu ba a san makomar wasu 'yan matan fiye da dari biyu ba da aka sace daga garin Chibok shekara guda da ta gabata.

Karin bayani