Amnesty ta zargi Syria da laifukan yaki

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Lugudan bama bamai a Aleppo ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula

Kungiyar Amnesty International ta zargi dakarun gwamnatin Syria da aikata muggan laifukan yaki a kullu yaumin a birnin Aleppo, ta hanyar yiwa yankunan da fararen hula suke ruwan bama bamai.

Kungiyar ta wallafa rahotan wasu lamura da shaidu suka tabbatar na irin barna da kuma jinin da aka zubar sakamakon wasu bama bamai da aka jefa a asibitoci da masallatai da kuma makarantu

Mutanen da suka tsira daga ruwan bama baman sun ce akwai gawarwakin yara da babu kawunansu a jikinsu birjik a kan tituna, yayin da wasu kuma, bangarorin jiki ake gani kawai.

Amnesty tace ruwan bama baman sun halaka mutane 3,000 a birnin Aleppo a bara, abinda ya tilastawa fararen hular boyewa a karkashin kasa.