An ci gaba da zanga-zanga a Burundi

Hakkin mallakar hoto

An cigaba da zanga-zanga a kasar Burundi bayan an dakatar da ita tsawon sa'oi 48.

Masu zanga-zangar na kira ga Shugaba Pierre Nkurunziza da kada ya tsaya takara a karo na uku.

Sun kakkafa shingaye tare da kona tayoyi a yankuna da dama na babban birnin kasar, Bujumbura.

An dai jibge jami'an 'yan sanda a yankun da dama na kasar domin tumkarar masu zanga-zangar.

Mutane shida ne suka mutu sakamakon zanga-zangar da aka yi a makon jiya.

Masu zanga-zangar sun yi kiran da a dakatar da ita ta kwanaki biyu domin makokin wadanda aka kashe sannan su sake tattara kayayyakin da suke bukata.