Mutane sun yi artabu da jami'an tsaro a Guinea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A farkon shekarar ma an yi zanga-zanga inda aka kashe mutane da dama

Masu zanga-zanga sun yi artabu da jami'an tsaro a Conakry babban birnin Guinea, lokacin da suke zanga-zangar adawa da sauya jadawalin zaben kasar.

A kalla mutane biyu ne suka ji rauni sakamakon harbinsu da aka yi.

Darurwan mata ne suka yi ta ihun nuna adawa da gwamnati yayin da suke yin maci zuwa cibiyar kasuwanci ta birnin amma sai jami'an tsaro suka tarwatsa su.

'Yan adawa dai sun ce saua jadawalin zaben ba zai haifar da da mai ido ga shugaba Alpha Conde ba.

A farkon shekarar nan ne aka kashe mutane da dama aka kuma ji wa wasu rauni a irin wannan zanga-zangar.