An tarwatsa masu zanga zanga a Isra'ila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Isra'ila

'Yan sanda a Isra'ila sun tarwatsa masu zanga zanga lokacin wata tarzoma a babban birnin kasar, Tel Aviv.

'Yan sandan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan daruruwan masu zanga zangar 'yan asalin kasar Habasha, wadanda suke korafin nuna wariyar launin fata.

Mutane fiye da 50 ne dai suka samu raunuka a tarzomar, akasarinsu 'yan sanda.

Tun da farko Yahudawa a Isra'ila 'yan asalin Habasha sun yi gangami na nuna bacin rai, bayan bayyanar wani hoton bidiyo dake nuna 'yan sanda suna dukan wani soja Ba'isra'ile dan asalin Habasha da baya sanye da kaki.

Firayiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya yi kiran a kawo karshen tarzomar, inda ya ce za a gudanar da bincike a game da dukkan zargin da ake wa 'yan sanda na nuna wariyar launin fata.