Isra'ila ta ci zarafin Palasdinawa a Gaza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin Isra'ila sun kashe Palasdinawa ba tare da bin dokokin yaki ba.

Wasu sababbin shaidu sun nuna cewa sojin Isra'ila ba su bi dokokin yaki ba a lokacin da suka kai hari a Gaza a bara.

Wata kungiyar Yahudawa da ke kare hakkin bil adama ce ta tattara shaidun bayan ta yi hira da sojin kasar fiye da 60.

Kungiyar, mai suna Breaking the Silence, wacce ta kwashe watanni takwas tana tattara shaidu daga sojin Isra'ilan da suka shiga yakin na Gaza, ta karyata ikirarin da Isra'ila ta yi cewa ta dauki matakin kare fararen hula a lokacin yakin.

Sojojin da kungiyar ta yi hira da su sun ce ba su dauki wani kwakkwaran matakin kare fararen hula ba.

Ita dai gwamnatin Isra'ila ta ce kungiyar ta Breaking the Silence ta hana ta ganin rahoton nata, lamarin da cewarta, ya sanya ba za ta mayar da martani ba.