Al'ummomin tafkin Chadi na cikin mummunan hali

Hakkin mallakar hoto FAROUK BATICHE AFP
Image caption Mahukuntan Jamhuriyar Niger sun ce sun bayar da umarnin ne domin samun damar kawar da Boko Haram.

A Jamhuriyar Nijar, al'umomin kasar da ke zaune a kusa da tafkin Chadi -- wadanda hukumomin kasar suka bai wa umarnin ficewa daga garuruwansu -- sun ce sun shiga cikin wata babbar masifa sakamakon kaurar da suke yi.

A ranar Litinin ne dai wa'adin da mahukuntan kasar ta Nijar suka bai wa fararen hular yankin na su fice daga garuruwa kamar su Karamgi da Gadira ke cika.

Sai dai wasu sun shaida wa BBC cewa mutane na mutuwa saboda yunwa da kishirwa saboda kaurar da suke yi, kuma babu motocin da za a kwashe su.

Hukumomin dai sun ce sun dauki wannan matakin ne domin bai wa sojojin kasar damar tunkarar mayakan Boko Haram ba tare da wani tarnaki ba.