Bam ya fada kan makarantar renon yara a Syria

Hakkin mallakar hoto SHAM NEWS NETWORK
Image caption Yara da dama sun mutu a harin da aka kai kan makarantar renon yara a Aleppo

Rahotanni daga birnin Aleppo na Syria sun ce gwamnati na ci gaba da harba bama-bamai a kan yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Wata babbar 'yan jarida a garin Zaina Erhaim, ta shaida wa BBC cewa daya daga cikin bama-baman ya fada kan wata makarantar renon yara da ke kusa da gidanta a ranar Lahadi da safe.

Ta ce ta ji ihun yara kuma ta ga masu aikin ceto suna kokarin zakulo yaran da suka mutu da wadanda suka ji rauni daga karkashin baraguazan gini.

Rikici yana kara kamari a birnin Aleppo a 'yan makonnin da suka gabata, inda dakarun gwamnati ke jefe manyan bama-bamai domin mayar da martani kan sabbin hare-haren da 'yan tawaye ke kai wa, wadanda su ma suke amfani da mugayen makamai.