Azabar da mutane suka sha a hannun 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Najeriya sun tserar da fiye da mutane 700 daga hannun 'yan Boko Haram

Azabar da mutane suka sha a hannun 'yan Boko Haram

Wadansu mata -- daga cikin mutanen da sojojin Najeriya suka ceto daga hannun 'yan Boko Haram a dajin Sambisa -- sun ce mayakan sun yi ta jifansu har sai da wasunsu suka mutu a lokacin da sojoji ke kubutar da su.

Matan sun ce mayakan Boko Haram sun fara jifansu ne a lokacin da suka ki guduwa yayin da sojoji suke durfafarsu.

Sojojin sun ce sun tserar da fiye da mutane 700 a makon jiya lokacin da aka kai hare-hare a kan mayakan kungiyar.

Matan dai sun ce mayakan sun kashe mutane da dama ta hanyar jifansu amma ba su san adadin mutanen ba.

'Masu juna biyu'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Salamatu Bulama ta ce tana daga cikin matan da 'yan Boko Haram suka jefa

Asama Umaru na daya daga cikin matan da suka tsira, ta shaida wa BBC cewa, "a wannan lokacin sojoji ba su gane cewa ba mu ne abokan adawar tasu ba, manyan motocinsu sun bi ta kan mata da yara da dama."

Matan sun ce a tun lokacin da aka sace su, mayakan sun kashe maza -- manyansu da yaransu -- a gaban iyalansu sannan suka dauke matan da sauran yara.

An tilasta wa da dama daga cikin matan sun yi aure.

Wata mata mai suna Lami Musa, mai shekaru 27, ta ce ta guje wa wannan kaddarar.

Ta ce "Da suka fahimci cewa ina da ciki, sai suka ce kafiri ne ya yi min ciki: suna nufin mijina, sai suka kashe shi.

"Kashi da rai"

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yara da yawa suna fama da tamowa

Lami ta ce mayakan sun gaya mata cewa "Da zarar kin haihu zamu aurar da ke ga kwamandanmu."

Cikin kuka Lami ta kara da cewa "Na haihu da daddare sai sojoji suka ceto mu washe gari da safe."

Sauran wadanda suka tsira sun ce mayakan kungiyar ba sa taba dauke ido daga kan su, ko da kuwa bandaki za su zaga.

Cecilia Abel ta bayyana yadda ake ciyar da su abinci sau daya kacal a rana, "Da rana ne kawai ake ba mu busasshiyar masara wacce sam ba ta yi kama da cimar dan adam ba."

Asabe kuwa kara cewa ta yi "A kullum sai an samu wadanda suka mutu a cikinmu kuma a gabanmu, don haka kullum cikin jiran tamu mutuwar mu ke yi." ----- Wakiliyar kamfanin dillancin labarai ta AP Michelle Faul, wacce ta ziyarci sansanin da mutanen suke ta shaida wa BBC cewa "Yara da yawa sun rame sun kwarjale sun zama kashi da rai."

Wani likita Muhammad Amin Suleiman, ya ce sai da aka yi wa jarirai da yara da dama Karin ruwa a asibiti.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne karo na farko da yara ke cikin lafiyayyen abinci tun bayan sace su

'Yan matan Chibok

Daga hirarrakin da aka yi, jami'ai sun ce yawancin wadanda aka tseratar din 'yan kauyen Gumsuri ne, wani kauye da ke kusa da garin Chibok.

Babu 'yan matan makarantar Chibok ko guda daya daga cikin mutanen da aka ceto din, wadanda mayakan Boko Haram suka sato daga makarantarsu shekara guda da ta gabata.