Ana gasar zanen barkwancin Annabi a Texas

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu daga cikin mutanen da suka halarci gasar

'Yan sanda a jihar Texas ta Amurka sun harbe wasu mutane biyu har lahira, wadanda suka bude wuta kan jami'in tsaro a wani wuri da ake gudanar da gasar nuna bajintar zanen-zanen barkwancin da aka kwaikwayi Annabi Muhammad (SAW).

Kungiyar American Freedom Defence Initiative, wadda ta shirya gasar, ta tanadi dala dubu 10 a matsayin babbar kyauta ga wanda zanen sa ya fi kwaikwayon Annabi Muhammad.

Mista Geert Wilders, dan kasar Holland da aka sani da kin jinin musulunci, shi ne babban mai jawabi a wajen gasar.

Jama'a a yankin kuma sun rufe sana'o'in su saboda harbe harbe.

Nuna hoto ko zanen batanci game da Annabi Muhammad (SAW) abu ne da yake bata ran Musulmai a wurare daban-daban.

A shekarar 2006 an ta gudanar da zanga zanga lokacin da wata jaridar kasar Denmark ta buga wani zanen barkwanci da ta nuna cewa Annabi Muhammad ne.

A watan Janairun wannan shekara ma, kimanin mutane 12 ne wasu 'yan bindiga suka kashe a kamfanin wata mujalla a Faransa wadda ta buga irin wannan zane na barkwanci.