Alkalin Burundi ya tsere daga kasar

Image caption Shugaban Kasar Burundi

Alkalin kotun da za ta yanke hukunci kan dacewa ko rashin dacewar sake tsayawa takarar shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi ya fice daga kasar kwanaki kadan gabanin yanke hukuncin.

Alkali Sylvere Nimpagaritse ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa ya fice daga kasar ne saboda yana fuskantar matsin lamba daga hukumomin kasar, ciki har da yunkurin hallaka shi, domin ya amince shugaba Nkurunziza ya tsaya takara a karo na uku.

Yunkurin da Mr Nkurunziza ke yi na ci gaba da mulki ya jawo zanga-zanga a kasar, kuma ya sanya ana fargabar sake barkewar yakin basasa, wanda aka kwashe shekara da shekaru ana yi a kasar.