Sarkin Saudiyya ya kori mai kula da baki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sarki Salman da Sarkin Morocco

Sarki Salman na Saudiyya ya kori shugaban sashen kula da baki na masarautar, bayan da wani hoton bidiyo ya nuna shi yana marin wani dan jaridar a lokacin zuwan Sarkin Morocco a birnin Riyadh.

An nuno Mohammed Al-Tobaishi ya mari dan jaridar a lokacin da Sarakunan biyu ke gaisawa a filin saukar jiragen sama na Riyadh.

An rarraba bidiyon a shafukan zumunta na zamani inda mutane suka yi ta kiran a dauki mataki a kan Al-Tobaishi.

Hanzarin da Sarkin ya yi na korar Al-Tobaishi na nuna irin yadda ba ya bata lokaci kan daukar hukunci a yayinda ya shafe kusan kwanaki 100 a kan mulki.