An lalata filin jirgin Sana'a da lugudan wuta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babban filin jirgin sama na Sana'a, Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta da suke yaki da 'yan tawayen Houthi a Yemen da su daina lugudan bama bamai a filin jirgin sama na kasa da kasa dake Sana'a.

Majalisar ta yi kiran ne a yayin da take shirin kai jami'an aikin jin kai Yemen daga Djibouti.

Jami'in Majalisar mai kula da ayyukan jin kai a Yemen, Johannes Van Der Klaauw ya ce filin jirgin yana da muhimmanci wajen kai kayan agaji da kuma kwashe wadanda suka samu raunuka.

Ya ce lugudan wutan ya lalata wasu bangarori na filin, kuma hakan yasa babu jirgi ba zai iya tashi ko sauka ba har sai an yi gyara.

Kasar Saudi Arabiya ta ce tana duba yiwuwar tsagaita wuta a wasu yankunan na Yemen domin bada damar kai kayayyakin dauki na jinkai.