Wasu maza za su sha dauri a Afghanistan

Image caption Wasu daga cikin mazan da aka samu da laifin kashe Farkhunda

Wata kotu a Afghanistan ta yanke wa wasu maza su hudu hukuncin kisa kan rawar da suka taka a kisan da aka yi wa wata mata a birnin Kabul a watan Maris da ya gabata.

Matar mai suna Farkhunda, wasu mutane suka yi mata duka kuma suka kashe ta bayan da aka yi mata zargin kona litafin Al kur'ani mai tsarki.

An wurgo gawarta daga saman wani gida inda wata mota ta taka ta daga bisani aka cinnawa gawar ta wuta.

An kuma yanke wa wasu mutane su takwas hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari yayinda kotun ta wanke wasu mutane su 18.

Sai dai wata mai rajin kare hakkin mata a kasar ta nuna rashin jin dadinta game da hukuncin kotun.