IS: Amurka ta ware tukwicin dala miliyan 20

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama

Amurka ta yi tayin bayar da ladar dala miliyan 20 a matsayin tukwici ga wadanda suka bayar da bayanai game da wasu shugabannin kungiyar IS 4.

Mutanen sune Abdulrahman Mustapha Al-Qaduli, da Abu Mohammed Al-Adnani, da Tarkhan Tayumurazovich Batirashvili da kuma Tariq Bin Al-Tahir Bin Falih Al-Awni Al-Harzi.

Al-Adnani shi ne kakakin kungiyar ta IS, yayin da Batirashvili kuwa, kwamandan yaki ne na kungiyar a arewacin Syria, shi kuwa Tariq Al-Harzi shi ne mai kula da masu kunar bakin wake na kungiyar.

A baya dama Amurkan ta yi tayin bada ladar dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayani a kan mutumin daya ayyana kansa a matsayin shugaban kungiyar IS, Abubakar Al-Baghdadi

Kungiyar IS ta ce ita keda alhakin kai hari a birnin Dallas na jihar Texas inda ake gasar nuna bajintar zanen barkwanci da aka kwaikwayi Annabi Muhammad (SAW).