Hoton yaran da ya sosa ran duniya

Hakkin mallakar hoto Na Son Nguyen
Image caption Hoton yaran da ya sosa ran duniya.

Wannan hoton yana cikin hotunan da aka fi yadawa ta hanyoyin sadarwa na zamani a lokacin da girgizar kasar Nepal ta auku a makon jiya.

Hoton yana nuna yara kanana biyu sun rungume juna; hoton yana da sosa rai kwarai da gaske, inda yarinyar ta rike dan uwanta tamkar dai shi ne kariya a gare ta, shi kuma yaron a firgice yake.

Hoton na da matukan sosa zuciya.

A cikin mako guda, hoton ya watsu sosai a shafukan sada zumunta irin su Facebook da Twitter, inda aka yi masa lakani da "yaro dan shekaru hudu yana kare kanwarsa 'yar shekara biyu a Nepal."

An yi ta kokarin nemo wadannan yara a cikin wadanda girgizar kasar ta shafa, har ma an bukaci taimako domin neman su.

An gano cewa an dauki hoton ne shekaru 10 da suka wuce a arewacin kasar Vietnam.

Wani dan kasar Vietnam mai suna Na Son Nguyen, shi ne wanda ya dauki hoton, kuma ya shaida wa BBC cewa, "Na dauki hoton ne a watan Oktoba na shekarar 2007 a wani kauye mai suna Can Ty, da ke lardin Ha Giang.

"Ina kan hanya ta sai na hango yaran suna wasa a kofar gidansu a lokacin da iyayensu ke aikin gona.

"Ina tsammanin yarinyar ba ta wuce shekaru biyu ba; ta saka kuka da ta ga cewa ni bako, shi ne dan uwanta -- wanda bai fi dan shekaru uku ba -- ya yi sauri ya rungume ta yana rarrashin ta.

"Abin tausayi ne kuma ya ba ni sha'awa, sai na dauke su hoto."

Na Son ya wallafa hoton a shafinsa na intanet kuma ya yi mamakin yadda masu amfani da shafin Facebook a Vietnam suka yi ta yada hoton shekaru uku da suka wuce da lakanin "Marayun da aka watsar".

Ya ce "Wasu ma har da kago labarai a kan yaran, wai mahaifiyarsu ce ta rasu, kuma mahaifinsu ya yi watsi da su."

Labarin bai tsaya a nan ba

Daga baya kuma Na Son ya sami labarin cewa an yi wa hoton lakani da "Marayun kasar Burma", wasu kuma suna kiran sa da suna "mutanen da yakin Syria ya shafa".

Na Son ya ce ya yi kokarin bayyana gaskiyar hoton kuma ya tabbatar wa duniya shi ne ya dauka, amma bai yi nasara ba.

Ya ce "wannan shi ne hotona da ya fi farin jini amma bayanin sa ba daidai yake ba".