Sankarau ta hallaka mutane 265 a Nijar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Ma'aikatar kiwon lafiya a jamhuriyar Nijar ta tabbatar da cewa ta samu karin dubban alluran riga-kafin cutar sankarau domin ci gaba da yi wa yara riga kafin da aka fara kwanakin baya.

A wannan karon dai, baya ga dalibai, shirin zai shafi dukan yara daga shekaru 2 zuwa 15 musamman cikin jahohin Yamai da Doso da kuma Tilabery wadanda a cikinsu ne cutar ta fi kamari.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta sankarau ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 265 a kasar ta Nijar a wannan shekarar.

Mutane fiye da 3,600 ne a yanzu haka suke fama da cutar sankarau a fadin kasar ta Nijar.

Kuma a cikin kwanaki 10 da suka wuce ne adadin ya rubanya.