An wargaza wasu sansanonin 7 a Sambisa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin mata da kananan yara da aka kubutar

Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta sun lalata sansanonin 'yan Boko Haram bakwai a dajin Sambisa, inda kuma suka kubutar da karin mata da kananan yara 25.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakakin rundunar, Kanar Sani Usman Kukah sheka, ya ce da safiyar ranar Laraba suka kubutar da mutanen sannan suka kashe wasu 'yan Boko Haram da dama.

A cewarsa soja daya ya mutu sannan wasu biyar suka samu raunuka a arangamar da aka yi da 'yan kungiyar ta Boko Haram

Sansanonin da aka lalata su ne sansanonin Alafa 1, 2, 3 da 4 da Rogo Fulani da Laraga Fulani da kuma wani sansani marar suna.

Kusan mutane 700 ne rundunar sojin Nigeria ta kubutar a cikin 'yan kwanakin nan daga dajin Sambisa kuma tuni aka kai wasu daga cikinsu jihar Adamawa domin kula da su.