Baga: An gurfanar da sojoji a gaban kuliya

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Babban hasfan dakarun Nigeria, Air Marshal Alex Badeh

Rundunar sojin Nigeria ta gurfanar da Birgediya-Janar Enitan Ransome- Kuti da wasu manyan jami'an soji hudu a gaban kotun soji bisa zarginsu da yin sakaci har mayakan Boko Haram suka kwace garin Baga a watan Janairu.

Mr Ransome Kuti, shi ne kwamandan dakarun sojin hadin gwiwa a lokacin da aka kai harin.

Lauyoyin da ke kare jami'an dai su ne suka wakilce su a lokacin sauraron karar a hedikwatar tsaron Nigeria a Abuja.

Ana tuhumar Mr Ransome-Kuti ne tare da Laftanal Kanal G.A Suru da Laftanal Kanal Haruna da kuma Manjo Aliyu.

A lokacin da mayakan Boko Haram suka kwace garin Baga sun hallaka daruruwan mutane sannan kuma suka kona daukacin gidajen garin.