Burundi: 'Karo na karshe da zan nemi tazarce'

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan Kasar Burundi sun ki amincewa da batun tazarcen Shugaban

Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya ce mulkin da yake nema a wani wa'adi na uku shine na karshe, a zabubbukan da za'a gudanar cikin watan Yuni a kasar.

A cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar, shugaban ya kuma dau alkawarin sakin wasu Yara kanana da aka kama nan take

An tsare Yaran a lokacin wata mummunar zanga zanga data barke sakamakon shawararsa ta sake tsayawa takara, wacce ta janyo cece-kuce, wacce kuma 'yan adawa suka ce ta saba tsarin mulki.

Shugaban Burundin ya kara da cewa za kuma a saki daruruwan mutanen da aka kama idan har aka tsaida zanga zangar.

Nan take dai Abokanan hamayyarsa, suka lashi takobin cigaba da zanga zangar

Wannan tashin hankalin dai ya sake jefa fargabar da ake cewa yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kawo karshen yakin basasar Burundi ka iya gamuwa da matsala