Ra'ayoyin 'yan ci rani a kan zaben Biritaniya

BBC ta zagaya sassa daban-daban na Biritaniya domin haduwa da mutanen da za su kada kuri’a a karon farko a babban zaben kasa, wadanda kuma ‘yan asalin wadansu kasashe ne. Wakilin BBC John McManus, ya duba dalilan da ke basu kwarin gwiwar kada kuri’ar.

‘Yan bi ranin Biritaniya sun fito ne daga kasashe daban-daban, amma suna da matsaloli iri daya a kan wannan zabe.

Mallakar gidaje masu saukin kudi na daya daga cikin wadannan matsaloli. Hauhawar farashi ya sanya matasa da dama ba sa iya mallakar gida.

Wannan matsala wacce kuma ta hadu da matsalar tsadar gidajen haya, su suka sanya al’amarin gidaje ya zamo babban abin dubawa a wannan zabe, inda dukkan jam’iyyun siyasar ke yin alkawarin gina gidaje yayin da wasu kuma ke cewa za su samar da dokar saukaka kudin haya.

Khalia Ismain, wata haifaffar London ce kuma daliba a jami’ar Manchasta ta ce tsadar da gidajen haya ke yi wata hanya ce ta azabtar da mutane sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin da basu suka yi sanadiyar ta ba.

Image caption Khalia Ismain

Akwai banbancin shekaru a harkar ilimi

Ba kamar can baya da gwamnati ke kula da karatun jami’a ta hanyar kudin haraji da ake karba ba, yanzu dalibai ne suke biyan kudin makaranta da kansu a Biritaniya, wadanda yawancin su sai sun karbi bashi kafin su iya biya.

Masu sukar lamura sun ce su kansu ‘yan siyasar da ke goyon bayan wannan dokar wadda aka samar da ita a shekara ta 2010, na daga cikin wadanda suka mori ilimi kyauta a baya.

Theo Chikomba, wani dalibi a jami’ar Manchasta haifaffen kasar Zimbabwe, ya yi magana da yawun tsararrakinsa da dama inda ya ce burinsu bai tsaya kan a soke biyan kudin makaranta da kuma dawo da tsarin da ake amfani da shi a baya ba kawai, suna so a yafe wa daliban basussukan da suka karba domin biyan kudin makarantar.

Image caption Theo Chikomba

Ana kuma samun karancin makarantu, inda iyalai da yawa basa samun damar zabar makarantar da suke muradi.

Moataz Attalah da Raniah Salamah, ‘yan asalin kasar Masar sun yi jira har na tsawon shekaru biyu domin su sami gida kusa da makarantar da suke so ‘yarsu ta yi.

Image caption Moataz Attalah da Raniah Salamah, ‘yan asalin kasar Masar da 'ya'yansu

Batun samar da inshorar lafiya shi ne kan gaba a cikin batutuwan da masu zabe za su yi la’akari da shi.

Amma wani mazaunin birnin Cardiff Ammar Rahim na ganin ya kamata a hade kamfanonin bayar da inshorar lafiya wuri guda domin ya samu hanyar samun magunguna ba tare da ya biya kudi ba.

Image caption Ammar Rahim dalibi a birnin Cardiff

A shekarar 2012 ne gwamnati ta rufe tsawaita bisar dalibai bayan sun kammala karatu, wadda ke bai wa daliban da suka zo Biritaniya daga wasu kasashen damar yin aiki a kasar na tsawon shekara biyu ba tare da wadanda suka basu aiki sun dauki nauyinsu ba.

Tabbas, akwai sauran batutuwa wadanda suke da muhimmanci ga wadanda ba ‘yan asalin Biritaniya ba, imma sabbin zuwa ne ko kuma wadanda iyayensu suka zo ci rani.

Ola Ouluwa Adekoya da Saint Owubokiri ‘yan Najeriya ne, sun jaddada bukatar a dawo da wannan tsarin bayar da bisa, suna masu cewa dalibai da dama sun mutu a ruwa a kokarinsu na biyo wa ta teku domin su sami aiki da manyan kamfuna.

Image caption Ola Ouluwa Adekoya dan Najeriya ne kuma dalibi a jami'ar Manchasta

Wani kwamitin gwamnati ya gano cewa yawan daliban kasashen ketare ya ragu a karo na farko cikin shekaru 29 sakamakon sauya tsarin.

Kamar yadda ake tsammani, wariyar launin fata da al’amuran shige da fice na da muhimmanci ga masu kada kuri’a da ba ‘yan asalin kasar ba wadanda suke zaune cikin al’umma ta turawa.

Wata daliba a jami’ar Birmingham 'yan asalin kasar Bangaladash mai suna Tasnim Miah, tana so a dinga ilimantar da yara dalibai ta fuskar addinai da al’adu daban-daban domin a samu saukin wariyar launin fata.

Image caption Tasnim Mia 'yar Bangladash a Biritaniya

Shi ma Kieran Carty, wanda ya fito daga yankin Caribbean, ya ce duk da cewa wasu daga cikin danginsa suna damuwa kan maganar harkar jami’an shige da fice, shi bai damu da hakan ba.

Image caption Matashi mazaunin Biritaniya

Mohamed Achaibou, mai shekaru 29 ya ce ya ga irin kyakkyawawan gudunmowowin da ‘yan ci rani suka bayar a Biritaniya cikin shekaru 10 da ya yi a kasar, yana mai cewa lallai su din ba karfen kafa bane ga kasar.

Image caption Mohamed Achaibu mazaunin London

A takaice dai, mafi yawan binciken da aka yi sun nuna cewa ‘yan ci rani suna bayar da gudunmowarsu wajen bunkaar tattalin arzikin kasar fiye da amfanin da suke samu.

Watakila babbar matsalar da Biritaniya ke fuskanta ita ce yadda yawan masu kada kuri’a ke raguwa ko yaushe.

Maryanne Mwiki, haifaffiyar Tanzaniya a da bata da ra’ayin kada kuri’a har sai lokacin da wani al’amari ya faru a makarantar da danta ke zuwa wanda ya yi sanadin neman taimako a wajen wani dan majalisar dokoki.

Image caption Maryanne 'yar Tanzaniya da 'ya'yanta

Anan ne ta fahimci cewa ita ma za ta iya taka ta ta rawar, kuma a wannan karon ta yi niyyar kada kuri’a a karon farko.

Lallai ‘yan siyasa na bukatar tuntubar Maryanne Mwiki domin sanin yadda za su karfafa gwiwar sauran masu kada kuri’a a kasar.