AU ta bukaci shugaban Burundi ya fasa tazarce

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane sun ce babu tazarce a Burundi

Kungiyar tarayyar Afirka watau AU ta bukaci shugaban kasar Burundi da ya janye aniyarsa ta sake neman wa'adin mulkin kasar karo na uku.

Ta kuma bukaci a dage zaben shugaban kasar zuwa wani lokaci nan gaba... saboda a cewarta yanayin da ake ciki bai dace da yin zabe ba.

Shugaba Pierre Nkurunziza na son ya yi tazarce a karo na uku a kan mulki, abin da ya janyo zanga-zangar Allah-wadai a kasar.

Mutum daya ya mutu ,wasu tara kuma suka ji raunuka a Bujunbura babban birnin kasar Burundi yayinda ake ci gaba da gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da matakin da shugaban.

A jawabinsa a ranar Laraba shugaba Nkurunziza ya ce idan aka zabe shi wa'adin da zai yi kan mulki shi ne na karshe.