Bill Gates na son rage mutuwar yara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bill Gates ya ce akwai bukatar rage mutuwar da kananan yara ke yi sakamakon cututtukan da ake iya yin riga-kafin su.

Hamshakin mai arzikin nan wanda ke da kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya bayyana shirinsa na kafa cibiyoyin kiwon lafiya a nahiyar Africa da Asia domin rage mutuwar kananan yara da yin rigakafin cututtuka irin su ebola.

Mr Gates ya shaida wa BBC cewa zai kafa cibiyoyin lafiya guda shida wadanda za su yi saurin gano cututtukan da za su iya barkewa ta yadda za a shawo kan su cikin gaggawa.

Mr Gates, wanda ya kafa gidauniyar The Gates Foundation da ke taimaka wa al'umma, ya ce zai ware $75m a matsayin kafin-alkalami domin kafa cibiyoyin kiwon lafiyar.

Mr Gates yana daga cikin manyan masu kudi a duniya wadanda ke bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban kasashe.