Shin ana gab da murkushe Boko Haram ne?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Nigeria na murnar kawar da Boko Haram

Idan har bidiyon da sojojin Nigeria suka nuna abu ne da za a duba da idon basira, to tabbas 'yan Nigeria na da hujjar da ke nuna cewa bisa dukkan alamu gwamnati na samun galaba a kan 'yan Boko Haram.

Dakarun Nigeria sun nuna wani bidiyo da ke nuna mayakan Boko Haram na gudu a cikin manyan motoci da babura a lokacin da sojojin saman Nigeria ke musu luguden wuta ta sama a dajin Sambisa.

A cikin mako guda kacal, sojoji sun kubutar da daruruwan mata da kananan yara bayan artabu da 'yan Boko Haram a dajin Sambisa.

Abin da hakan ke nufi shi ne sojojin Nigeria ba wai garuruwa kadai suka kwace ba a yankin arewa maso gabashin kasar, har da rutsa 'yan Boko Haram din a cibiyarsu da suka boye.

'Luguden wuta a Sambisa'

Nuna wannan hujja alama ce da ke nuna cewar akwai nasara tare da dakarun Nigeria a yaki da Boko Haram.

Kafin wannan lokacin, 'yan Boko Haram karkashin jagorancin Abubakar Shekau sun tafka ta'asa inda suka hallaka dubban mutane tare da azabtar da wasu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin matan da aka kubutar daga dajin Sambisa

Shekau a sakonsa na karshe ya yi mubaya'a ga shugaban kungiyar IS, Abubakar al-Bagadadi.

Wannan nasarar a kan Boko Haram ta kara zaburar da jami'an tsaron Nigeria a daidai lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan ke shirin kamalla wa'adin mulkinsa a karshen watan Mayu.

Janar Muhammadu Buhari mai jiran gado ya sha alwashin kawar da Boko Haram idan ya hau gadon mulkin kasar a karshen wannan watan.