Ana yin zaben 'yan majalisa a Biritaniya

Image caption An bude runfunan zabe a Birtaniya

Miliyoyin 'yan Biritaniya suna kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki da a ke gani ya fi ko wanne zafi a shekaru da yawa.

'Yan majalisar dokoki 650 ne za a zabe, kuma kimamin mutane miliyan 50 ne za su yi zaben.

Za a gudanar da zaben ne a rumfunan zabe dubu 50 a fadin kasar.

Binciken jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa babu wata jam'iyya daga cikin manyan jam'iyyun siyasar kasar da take da tabbacin samun kujeru mafi rinjaye da za ta kafa gwamnati.

A wasu biranen da suka hada da Bedford, da Copeland da Leicester, da Mansfield da Middlesbrough da kuma Torbay, za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin ne tare da na magadan gari.

Wasu mutanen ma tuni suka riga suka kada nasu kuri'un ta hanyar akwatunan gidan waya.

Manyan batutuwan da suka fi jan hankalin jagororin manyan jam'iyyun siyasar Biritaniya a yakin neman zaben su ne tattalin arziki, da rashin aikin yi, da kasancewar Biritaniya cikin Tarayyar Turai, da batun zaman baki a kasar, da kuma batun haraji.