Mummunan cunkoson motoci a Lagos

Image caption Wasu mutane sun koma gida sun fasa zuwa wurin aiki a Lagos saboda cunkoso

Masu abubuwan haya a birnin Lagos cibiyar kasuwancin Nigeria sun shafe awoyi a kan tituna ba-gaba ba-baya sakamakon cunkoso a kan hanyoyi.

Bayanai sun ce lamarin ya fi muni a manyan titunan birnin da ke unguwannin Apapa da Lagos Island da Oshodi da kuma Victoria Island.

Wakilin BBC a Lagos, Umar Shehu Elleman ya ce ya shafe awa biyar a kan hanyarsa ta zuwa Ijesha-Surulere daga unguwar Ikoyi, sabanin mintuna talatin da ya saba yi daukarsa tsakanin unguwannin biyu a baya.

Rahotanni sun ce an samu cunkoson ne sakamakon lodin da manyan motocin dakon mai ke yi daga depo-depo inda za su kai man zuwa sassa daban-daban na kasar.

Lagos ce cibiyar kasuwancin Nigeria kuma an saba fuskantar cunkoson abubuwan haya a hada-hadar yau da kullum a birnin.