SNP ta yi nasara da gagarumin rinjaye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kusa a jam'iyyar Labour Douglas Alexander ya sha kaye a hannun Mhairi Black ta SNP

Bayan kammala kidaya dukkan kuri'un da aka kada a yankin Scotland, jam'iyyar 'yan kishin kasa ta Scottish National Party, SNP, mai fafutukar neman 'yancin kai daga Burtaniya, ta yi samu kujeru 56 a cikin 59 na yankin.

Jiga-jigan jam'iyyun Liberal Democrat da Labour a yankin, cikin har da Sakataren Baitul Mali Danny Alexander da daya daga cikin jagororin yakin neman zabe na jam'iyyar ta Labour, Douglas Alexander, sun rasa kujerunsu.

Douglas Alexander ya sha kaye ne a hannun wata daliba 'yar shekara 20, Mhairi Black.

Shi ma shugaban jam'iyyar Labour a yankin, Jim Murphy, ya rasa kujerarsa.

Sakamakon wannan zabe dai ka iya yin babban tasiri a kan makomar Burtaniya a Tarayyar Turai da ma hadin kan kasar.

David Cameron ya yi alkawarin sake tattaunawa dangane da dangatakar Burtaniya da Tarayyar ta Turai da nufin sauya matsayin kasar, da kuma gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan ko kasar za ta ci gaba da zama a tarayyar.

Nasarar da jam'iyyar SNP ta yi a yankin Scotland za ta kara matsin lamba a kan sake gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan 'yancin kan yankin, duk da wadda aka yi bara wacce sakamakonta ya nuna mutanen kasar na son ci gaba da kasasncewa a cikin Burtaniya.