Ana bukukuwan kare yakin duniya na biyu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu tsofaffin sojojin da suka yi yakin duniya na biyu a birnin Kiev na Ukraine

A fadin Turai ana bukukuwan cika shekaru 70 tun bayan da dakarun Jamus na Nazi suka mika wuya, ga sojin taron dangi, lamarin da ya kawo karshen Yakin Duniya na Biyu.

A London, tsoffin sojoji za su jagoranci yin tsit da addu'o'i na minti biyu a kabarin dogon yaro, sannan za a yi bukukuwa a karshen mako.

A daren Alhamis, shugabannin kasashen Turai da dama sun halarci wani bikin a birnin Gdansk na kasar Poland, inda sojojin Nazi suka kai harin farko na yakin.

Tun kafin fara bikin, Shugaba Petro Poroshenko na Ukraine ya yi gargadin cewa, hadewa ko mamaye yankin wata kasa da sunan ba da kariya ga tsirarun kabilu, da rufe ido idan an aikata hakan, ka iya barazana ga hadin kan Turai.