Saudiyya za ta tsagaita wuta a Yemen

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudiyya ta shafe makonni tana kai hare-hare kan mabiya Houthi a Yaman

Kasar Saudiyya ta gabatar da wani shirin tsagaita bude wuta a Yemen, domin kungiyoyin agaji su samu damar kai kayan agaji ga fararen hula da ke kasar.

Sai dai da ya ke magana da 'yan jarida bayan da suka kammala tattaunawa da jami'an gwamnatin Saudiyya, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya ce za'a fuskaci jinkiri kafin shirin ya soma aiki.

Mr Kerry ya ce, "Yanzu haka, ana kan aiki a kan yadda za'a aiwatar da shirin, domin a tsara abubuwan da shirin ya kunsa da kuma ranar da bangarorin biyu za su soma aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta."

Rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta ta shafe makwanin tana kai hare-hare wuraren da ke karkashin ikon mayakan 'yan tawaye mabiya Houthi.