WHO za ta ayyana Liberia ta rabu da Ebola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kwashe kwanaki 42 ba a samu wanda ya kamu da cutar Ebola a Liberia ba

Nan gaba a yau Asabar ne ake sa ran Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, za ta bayyana cewa babu sauran cutar Ebola a Liberia, bayan an tabbatar da cewa ba a samu wani wanda ya kamu da cutar ba a kwanaki 42.

Sai dai WHO ta ce yanzu ba lokaci ne da za a sakankance ba; don kuwa har yanzu akwai cutar ta Ebola a makwabtan kasar ta Liberia, Guinea da Saliyo.

Fiye da shekara guda da ta wuce ne kasar ta Liberia ta ba da rahoton kamuwa da cutar a karo na farko bayan cutar ta yadu daga Guinea.

Cutar ta Ebola dai ta kashe mutane fiye da dubu goma sha daya a Yammacin Afirka.