Taliban ta dauki alhakin harbo jirgi a Pakistan

Image caption A kalla mutane shida ne suka rasa rayukansu sakamakon fadowar jirgin

Kungiyar Taliban da ke Pakistan ta fitar da wata sanarwa inda ta ce ita tayi amfani da makamai da ke kakkabo jirage ta harbo jirgin soji mai saukar ungulu da ke dauke da jakadun kasashen waje.

Rundunar sojin Pakistan ta ce jakadun kasashen Norway da na Philippines na daga cikin mutane shidan da suka rasa rayukansu bayan da jirgin ya fada kan ginin wata makaranta da ke arewacin kasar.

Matuka jirgin biyu da kuma matan jakadun Malesiya da Indonesiya na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a cikin jirgin.

Daga cikin mutane 13 da suka tsira da ransu a hadarin sun hada da jakadun wasu kasashe wadanda suka samu munanan raunuka.

Kungiyar Taliban ta ce ta so kai harin ne kan Firai ministan kasar Nawaz Shariff saboda yana tafiye-tafiye a jirage masu saukar ungulu daban-daban.