Kamfanin Ericsson ya kai karar Apple

Image caption Kayan Apple da yawa suna amfani da fasahar Ericsson ne

Kamfanin Ericsson ya shigar da kara a kan kamfanin Apple kan zargin kin biyansa kudin lasisin amfani da fasaharsa.

Kamfanin kera kayan sadarwar na Ericsson na Sweden, ya ce, kamfanin Apple yana ci gaba da amfani da fasaharsa duk da cewa ba shi da lasisin izinin yin hakan.

Ericsson, ya ce, ya nemi ya tattauna kan batun yarjejeniya da Apple, amma ynzu wannan lokaci ya wuce.

Kamfanin ya shigar da karar ne a kasashen Birtaniya da Jamus da kuma Netherlands.

A nasa bangren Apple har yanzu bai ce komai ba game da karar.

Hakkin mallakar hoto x
Image caption Idan Ericsson ya yi nasara a shari'un Apple zai rika biyan sa kusan dala miliyan 725 a shekara.

Shugaban sashen hakkin mallaka na Ericsson, Kasim Alfalahi, ya ce, ''ana amfani da fasaharmu a kayayyakin sadarwa da yawa na yanzu.

Ya kara da cewa, ''shekara biyu ke nan ake wannan dambarwa ta shari'a, kuma ina d kwarin gwiwa kotunan za su taimaka wajen kawo karshenta da adalci.''

Ericsson yana da hakkin mallaka na fasahohi sama da 35,000 na wayoyin salula da kayan sadarwa na tafi-da-gidanka.

A 2014 kamfanin Samsung ya biya Ericsson dala miliyan 650 domin kawo karshen dambarwar amfani da wata fasaha da ya mallaka.