Liberia ta rabu da Ebola

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa babu sauran cutar Ebola a Liberia.

Jami'anta sun ce ba'a sami wani sabon bullar cutar ba a tsawon kwanaki 42, wanda ya ninka adadin kwanakin da kwayar cutar ke iya bayyana.

Shugabar Liberiar Ellen Johnson Sirleaf ta shaida wa BBC cewa tana farin ciki da aka ga bayan cutar a kasar baki daya.

Ta ce: "Ya al'ummar duniya a yau ina farin ciki tare da godiya cewa mun sami sanarwa a hukumance daga Hukumar Lafiya ta Duniya, an kakkabe cutar ebola a Liberia.

"Ga kasa da kuma jama'ar da suka sha wahalar wannan mugunyar cuta, wannan sanarwa muhimmiya ce ga daukacin 'yan Liberia."

Karin bayani