Zanga-zanga: An kama mutane 17 a London

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu zanga-zangar sun fusata ne da nasarar jam'iyyar Conservative

'Yan sanda a Burtaniya sun kama mutane goma sha bakwai a tsakiyar birnin London yayin wata zanga-zanga wadda daruruwan masu adawa da matakan tsuke bakin aljihu suka yi.

An yi wa 'yan sanda biyar rauni a hatsaniyar da ta auku a kofar fadar fira ministan kasar.

An yi ta jifa da da bam din kwalba sannan an barnata wani ginin tunawa da tsoffin sojoji.

Fira ministan kasar, David Cameron, wanda aka sake zaba ranar Alhamis, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da rage kashe kudi da nufin rage gibin kasafin kudi.

Karin bayani