Barayi sun yi awon gaba da shanu 600 a Ibi

An kai hare-haren ne a kauyyukan Tapga da kuma Damfar.

Sakakataren kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a karamar hukumar Ibi Malam Saidu Yupka, ya tabbatar da cewa 'yan bindigar sun sace shanu 500 a kauyen Tapga, amma daga bisa aka ci karfinsu aka kwace kimanin 300 amma sun arce da dabbobin kimanin 200.

Barayin dabbobin sun kuma sace wasu shanun kimanin 400 a kauyen Damfar duka a cikin karamar hukumar ta Ibi a jihar Taraba.

Fulani makiyayan dai su kan zargi 'yan kabilar Taroh ne da yawan satar shanun, zargin da 'yan kabilar Taroh din kan musanta.

Matsalar satar shanu dai na daya daga cikin abubuwan dake haddasa rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini a yankunan kan iyakar jihohin na Taraba da Filato wanda kan kai ga hasarar rayuka.