An kai hari gidan tsohon shugaban Yemen

Image caption Mayaki yana tashi daga gidan tsohon shugaban kasar Yemen, Ali Abdullah Sale

Dakarun Yemen din da suka yi tawaye suka kuma taimaka 'yan tawayen Houthi suka kwace galibin yankunan kasar sun amince da wata shawarar tsagaita bude wuta har tsawon kwanaki biyar wadda Saudiyya ta gabatar.

Wani mai magana da yawun dakarun, Kanar Sharaf Luqman ya ce yarjejeniyar tsagaita bude wutar za ta fara aiki ne ranar Talata, ko da yake babu tabbas a kan ko yana magana ne da yawun daukacin mayakan 'yan tawayen.

Wannan na zuwa ne yayin da dakarun da kasar Saudiyya ke yiwa jagoranci suka kai hari ta sama a kan gidan tsohon shugaban kasar ta Yemen, Ali Abdullah Sale, a Sanaa babban birnin kasar.

Tsohon shugaban kasar, wanda ke kawance da 'yan tawayen Houthi, ba ya gidan lokacin da aka kai harin.

Tun da farko dai wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Yemen, Johannes Van Der Klaauw, ya zargi dakarun da barin bama-bamai a kan mai uwa da wabi.

Wata jami'ar kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières, Teresa Sancristóbal, tana birnin Saada na arewacin kasar lokacin da aka kai wani hari ranar Juma'a.

A cewar ta, "Muna jin bama-bamai kusan ashirin ne muka ji kararsu a kusa da asibitin da muke. Yanzu dai tituna ba kowa".