Gwamnatin Kebbi da NEMA na takaddama

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan gudun hijra fiye da 2,000 ne aka kai Sokoto

A Najeriya, takaddama ta kunno kai a tsakanin Hukumar ba da Agajin Gaggawa, NEMA, da gwamnatin Jihar Kebbi a kan 'yan gudun hijira.

Hukumar ta NEMA ta zargi gwamnatin da yi wa batun 'yan gudun hijira 1,600 'yan asalin Jihar Kebbi wadanda suka taso daga Karanga na Jamhuriyar Nijar riko sakainar kashi.

'Yan gudun hijirar dai na jibge ne a wajen birnin Sokoto.

Gwamnatin dai ta musanta wannan zargi, tana mai cewa ba kamshin gaskiya a cikinsa.

Mataimakin jami'in hukumar NEMA mai kula da shiyyar Sokoto, Thickman Tanimu, ya ce tun ranar Alhamis suka sanar da hukumomin Jihar Kebbi game da 'yan gudun hijirar.

"Tun da muka yi waya {gwamnatin}, sakataren gudanarwa ya zo ya ga mutanen nan...lokacin ma ba su fi 400 ba, ya dauki wayarsu ya tafi da nufin zai je ya nemo motoci.

"Daga baya sai na kira shi na gaya mai...mutanensu sun ma fi 1,500...ya ce mu jira su zuwa {sallar} Juma'a. Amma har aka kai ga maraice ba su zo ba.

"Daga baya da na kira shi sai ai gwamna ya ce ba zai yiwu a ce mutane mutane fiye 1,500 'yan Kebbi ba ne, saboda haka sai sun kafa kwamiti an tantance su sannan a karbe su...."

Sai dai kuma mai magana da yawun gwamnan jihar, Alhaji Abdullahi Musa Argungu, ya ce wannan labari ko alama ba gaskiya ba ne.

"Hukumar NEMA ba su yi mana adalci ba--sun san ba su zo sun kawo mana labarin ba sai ranar Juma'a, lokaci ya kure...ko da suka zo kuma ba su nemi ganin gwamna sai wajen magariba".

Alhaji Abdullahi ya kuma ce tuni gwamnan ya bayar da umarni a dauki mataki kuma ranar Litinin za a je a kwashe mutanen.

A farkon watannan ne dai hukumomin Jamhuriyar Nijar suka umarci fararen hula su fice daga tsibirin Karanga, inda mutanen ke zaune, don bai wa sojoji damar tunkarar mayakan Boko Haram wandanda suka aki hari a can suka kashe sojoji kusan hamsin.